Wani mahaifi mai shekara 73 a kasar Kenya, ya kai dan shi kara a gaban Kotu yana neman Kotu ta tilasta dan shi ya dinga biyanshi kaso 20 daga cikin albashinsa kowane wata domin ya dinga kula da kanshi da kudin. Shafin isyaku.com ya ruwaito.
Mahaifin, mai suna Gideon Kisira Cherowo, dan asalin garin Biirunda ne da ke gundumar Trans Nzoia County, ya yi korafin cewa danshi mai shekara 48-Washington Chepkombe Cherowo ya yi watsi da shi bayan ya matukar taimaka wa rayuwarsa tun yana yaro har ya girma zuwa wannan matsayi na mai Takardun karatun matsayin Digiri.
A Takardun da aka gabatar a gaban babban Kotun Kitale, Mzee Cherowo, ya ce dan shi baya aika masa da kudi domin biyan bukatun yau da kullum duk da cewa yana aiki a sashen hukumar jiragen sama na kasar Kenya wanda suke da albashi mai kyau.
Mzee Cherowo ya ce a cikin yayan shi guda hudu, Washington ne kadai ya samu aiki a halin yanzu.
Mahaifin ya ce:
"Na yi amfani da duk kadarorina domin in ba shi kariya domin ganin ya zama mutumin kirki a cikin al'umma domin ya taimake mu. Yanzu haka ni da matata muna cikin wani mawuyacin hali duk da yake muna da dan da muka haifa da yake aikin albashi".
" Na sayar da fili na a garin Cheptais da ke Bungoma na biya masa kudin makaranta daga Pramare zuwa Jami'a. Kazalika na bashi wani fili na mai girman rabin hekta. Hatta sadakin aurensa ni na biya da shanu guda hudu da wasu kudi da dama da ba zan iya tuna yawansu ba a halin yanzu".
" Ina rokon Kutu tunda yana da albashi mai kyau, Ina bukatar ya dinga bani kaso 20 daga cikin albashinsa a matsayi na na mahaifinsa da na yi masa hidima lokacin da yake yaro karami".
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI