Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar 'yan Najeriya 10,000 aiki a matsayin jami'an 'yan sanda.
Hakan na daga cikin kokarin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro da suka addabi yankuna daban-daban na kasar.
Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an dauki jami'an ne a fadin jihohi 36 na kasar da babbar birnin tarayya.
Ya kuma bayyana cewa an zabi mutane goma-goma daga kowani kananan hukumomi 774 na kasar
Har wa yau, ya bayyana cewa tuni aka aikewa zababbun jami'an sako ta adireshin imel da suka yi rijista da shi.
Bashir ya wallafa:
"Kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi, hukumar 'yan sanda Najeriya (NPF) ta dauki 'yan Najeriya 10,000 aiki a matsayin jami'an 'yan sanda a fadin jihohi 36 na kasar da babbar birnin tarayya Abuja, domin magance matsalolin tsaro a wasu yankunan kasar.
"An zabi mutane goma daga kowani kananan hukumomi 774 na kasar, kuma tuni aka sanar da su ta adireshin imel da suka yi amfani da shi wajen neman aikin. "An gode Baba!"
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka