An harbe wani hakimi mai suna Alhaji Umaru Bawan Allah a wani hari da aka kai a unguwar Gada dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Daily Trust ta tattaro cewa an kashe wasu mutane biyar a harin wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Laraba
Mazauna yankin sun ce wasu ‘yan bindiga da dama ne suka afkawa al’ummar garin da misalin karfe daya na dare, inda suka shiga gida-gida, suka sace mutane kana suka harbe wasu har lahira.
Yan ta'addan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba, da suka hada da mata da kananan yara, wadanda akasarinsu aka kama a lokacin da suke kokarin tserewa.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:
Duk da haka, tare da hadin gwiwar 'yan banga na yankin da jami'an tsaro an ceto mutanen da aka sace."
“An gano 'yan bindigan ne a wani wuri kusa da yankin Karakkai. Jami’an tsaro sun taru inda ‘yan banga na yankin suka taimaka wajen tare hanyar.
"Bayan wani mummunan artabu, 'yan bindigar sun yi bar wadanda aka sace, watakila saboda ba su da yawa."
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Source: Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka