Gwamnatin jihar Niger ta mayar da Almajirai 104 zuwa jihar Sokoto ranar Litinin 20 ga watan Disamba. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.
Amajiran yan shekara 4 zuwa 10 an gano su ne tare da wani Malaminsu su a wata motar Trela a garin Maikunkele, yayin da suke gaf da shiga jihar Niger daga jihar Sokoto.
Malamin ya ce zai kai su makarantar Allo ne da ke Angwan Biri a karamar hukumar Bosso inda yaran za su zauna domin su yi karatun.
Darakta janar na ma'aikatar kula da hakkin Yara, Niger State Childs Rights Agency, Maryam Kolo ta ce babu tausayi kan yadda aka saka yaran a motar Trela a cikin irin wannan yanayin sanyi tun daga jihar Sokoto har zuwa jihar Niger.
Ta ce an mayar da yaran zuwa jiharsu ta Sokoto ne bisa la'akari da tabbatar da dokar Gwamnatin jihar Niger na hana barace-barace a fadin jihar da kuma ayyukan Almajiranci.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari