Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya ce, bai yarda da tsarin sauya wa 'yan ta'adda hali ba, ya kara da cewa hanyar da ta fi dace wa a bi da su kawai shine su 'tafi su gamu da Allah'.
Gwamnan ya bayyana matsayarsa kan batun ne a ranar Talata yayin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawa da Shugaba Muhamamdu Buhari, The Cable ta ruwaito.
Ya kai ziyara gidan gwamnatin ne domin yi wa Shugaba Buhari bayani kan harin baya-bayan da yan ta'adda suka kai inda suka kashe mutum 40 a Kaduna.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya yi wa gwamna El-Rufai rakiya zuwa gainin Buhari.
Ya ce: "Babu wani abu mai suna tubabbun yan ta'adda. Dan ta'addan da ya tuba kawai shine wanda ya mutu. Niyyar mu shine mu kashe su (yan ta'addan), su tafi su ga Allah."
El-Rufai ya ce an sun san inda yan ta'addan suke boye wa amma sojoji suna duba fararen hula da ka iya mutuwa ne idan an ce za a far musu a inda suke.
Gwamnan ya ce akwai yan ta'adda iri uku: Yan Boko Haram, Yan Bindiga da Yan Kungiyar IPOB kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ya ce ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda da aka yi a baya bayan nan ya bawa sojoji daman ragargazarsu da yakarsu.
El-Rufai ya bakuci shugaban kasa ya sake tura jami'an tsaro uwa Kaduna domin samun daman magance matsalar.
Ya yi kira ga jami'an tsaro su kara zage damtse wurin ragargazan 'yan ta'addan.
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI