Fusatattun matasa a birnin Awka na jihar Anambra sun banka wa wasu barayin wayar salula wuta suka kone kurmus a karshen mako. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Lamarin ya faru a Regina Caeli Junction, kan tagwayen hanyar Awka zuwa Onitsha.
Rahotanni na cewa an bi barayin yawar ne kayan sun kwace wayar a wajen wani mutum kuma aka kama su.
A biranen Onitsha, Nkpor da Obosi na jihar Anambra, akan banka wa barayi wuta ne a kone su kurmus domin ya Zama darasi ga wadanda ke niuyar aikata irin wannan laifi.
Shelkwatar yansandan jihar bata ce uffan ba dangane da lamarin kafin lokacin rubuta wannan rahotu.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari