Yan bindiga sun kashe matafiya 6 suka sace wasu matafiya da dama a kan hanyar Kaura Namoda zuwa Shinkafi a jihar Zamfara. Daily trust ta ruwaito.
Mazauna yankin sun shaida wa Jaridar Daily trust cewa Yan bindigan sun kone wasu matafiya a cikin motoci da ransu, lamari da ya sa zaro gawakin matafiyar ya yi wuya.
Sun ce Yan bindigan karkashin jagorancin kasurgumin dan bindiga Bello Turji sun fadada farmaki a yankunan Shinkafi da Kaura Namoda bayan jiragen yakin sojin sama na Najeriya NAF ya yi luguden wuta da ya yi sanadin mutuwar wata Innar Turji tare da mijinta kuma aka halaka sojinsa da dama.
Jaridar ta ce wani mazauni yankin ya shaida mata cewa Yan bindigan sun dakile wani wuri a hanyar tsakanin Kwanar Jangeru da Moriki, sakamakon haka jama'a suka daina bin ta wannan hanyar saboda tsoron lafiyarsu, lamari da ya sa samo gawakin wadanda Yan bindigan suka kashe ko suka kone da ransu ya yi wuya.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka