Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano


Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi magana a game da sabaninsa da shugabannin jam’iyyar APC da ke tare da gwamnati. 

A wata hira da aka yi da Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau a BBC Hausa a ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021, ya bayyan yadda abin yake. 

A wannan tattaunawa, Shekarau ya yi maganar yadda suka zauna da Tinubu da abin da suka yi magana a kai, da kuma zargin ya ci amanar ‘Yan G7. 

Abin da ya faru shi ne tun sama da sati guda, (Bola Tinubu) ya neme ni ta waya, ya nemi mu hadu. - Shekarau. 

“Kuma ba wani bakon abu ba ne, mun saba haduwa tun ba yau ba, tun da muka yi aikin maja (hadewa jam’iyyun hamayya) shekaru takwas da suka wuce.” 

“Na fada masa cewa ni ina Kano, na ce idan na dawo Abuja sai mu hadu. Amma sai yace ya na da wani uzuri a Abuja, sai wani abu ya kai ni Legas, mu ka hadu.” 

Me muka tattauna da Tinubu - Shekarau (Tinubu) ya ce ya naso ya ji gaskiyar al’amari, wai mu na rigima ni da gwamnan Kano? – Shekarau. 

“Na ce ba rigima ce tsakanin da Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje ba, rigima ko jayayya ce da muke yi da shugabancin jam’iyyar APC. 

“Kuma abin da mu ke cewa shi ne ba a ba ‘ya ‘yan jam’iyya dama a kana bin da ya shafi jam’iyya. “Yace gwamna ya fada masa labari daga bangarinsa, zai so ya ji na mu. 

Na fada masa asalin rigimar da yadda ta kaya, har aka zo hukuncin kotu.” G7 da shirin zaben 2023 Kun ji cewa tsagin masu adawa da gwamnatin Kano sun ce ba su san an yi wannan haduwar ba. 

Da aka tambaye shi ko ragowar ‘yan tsaginsa na G7 ba su san da wannan zama ba, sai Sanatan yace wannan ba gaskiya ba ne, tare da yawun saura aka yi zaman. 

A game da ko zaman na da nasaba da marawa Tinubu baya a zaben 2023, sai Shekarau yace babu batun zuwa goyon baya, akasin rahoton da aka ji a safiyar Talatar nan. 

Source: Legit.ng 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN