Tsohon Gwamnan jihar Edo Lucky Igbinedion yanzu haka yana zaman makoki da jimamin mutuwar mahaifiyarsa Madam Oredola Igbinedion ranar 2 ga watan Disamba. Shafin isyaku.com ya samo.
Rahotanni sun ce tsohuwar yar shekara 85 ta rasa ranta ne bayan yar aikin gidanta ta shake ta har ta mutu a gidanta da ke Ugbor, a GRA, da ke cikin Birnin Benin babban birnin jihar Edo.
Kazalika isyaku.com ya samo cewa yar aikin gidan wacce ta fito daga jihar Cross River, ta yamutse kayakin gidan ta sace gwala-gwalai da sauran kayakin alfarma da zinari na tsohuwar kafin ta tsere.
Sai dai wani daga cikin iyalin tsohon Gwamnan ya ce an sanar da jami'an tsaro kuma sun fara gudanar da bincike domin kama yar aikin gidan.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka