Babbar magana: Shehin malami ya magantu, ya ce mata su daina yiwa mazajensu girki da aikin gida


Shahararren malamin addini a kasar Kenya, Sheikh Yusuf Hassan ya shawarci maza da su dauki ’yan aikin gidajensu domin su rika kula da ayyukan gida ga matayensu.


Da yake magana yayin wata tattaunawa kan iyali a gidan talabijin na NTV, Shehin ya bayyana cewa addini ya hana matan aure rubanya ayyukan gida da kula da mazajensu.

Ya yi jayayya cewa matan da ke aikace-aikacen gida suna tsufa da wuri.


Yace:


"Bai kamata mata su yi girki ko tsaftace gida ba, kada a saka su aiki kamar jakkai, shi ya sa wasu matan ke saurin tsufa."

Mata su mai da hankali kan ayyukan dakunan kwana da kula da miji

Ya kara da cewa ya kamata mata su kasance aikinsu kadai ba da soyayya ga mazajensu.


Ya kara da cewa:


"Matar aure kamata ya yi ta yiwa mijinta hidima a kan gadon, aikinsu kadai kenan, bai ma kamata ta yi shimfidi a gadon ba."

Muhawarar dai ta jawo cece-kuce daga masu amfani da shafukan sada zumunta inda wasu ke adawa da batun nasa yayin da wasu suka amince da hakan.


Martanin jama'a

Ga kadan daga cikin martanin, kamar yadda kafar labarai ta kasar Kenya, tuko.co.ke ta tattaro.


Samanta Darleen yayi sharhi da cewa:


"Gaskiya! Ina zaune a Saudiya mata kawai suna shafe lokutansu ne a gado wah."

Oliver Wanjala ya ce:


"An halicci mace daga hakarkarin namiji don ta zama mataimakiya ce kawai. Wannan yana nufin wanda ya yi niyyar taimakawa, zai iya yanke shawarar ba zai taimaka ba kwata-kwata, da son ransa. Amma kan haihuwa, umarnin Allah ne a hayayyafa shi ya sa batun gado ya zama shine kadai wajibi ga mace. Ba za ta iya guje wa hakan ba. Don haka na yarda."

Julius Marereh ne ya rubuta


"Wannan shirme ne kololuwarsa."

Ben Torres yayi sharhi:


"Wannan zai karfafa kasala. Da yawan tsammani."

Hukumar Hisbah ta wajabta kwasa-kwasai kan zamantakewar aure ga masoya gabanin aure

A wani labarin, Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta ce daga yanzu za ta bukaci dukkanin masoyan da suke shirin aure mabiya addinin Musulunci a jihar da lallai sai sun halarci kwasa-kwasai kan zamantakewar aure domin tabbatar da sun cancanci auren kafin a daura musu aure.


Babban Kwamandan hukumar Harun Ibn-Sina, ya fada a ranar Alhamis cewa bijiro da wannan tsarin ya zama wajibi lura da yawaitar matsalolin muruwar aure tsakanin ma’aurata a jihar, rahoton SR.


Ya kuma nunar da cewa dole ne sai masoyan da ke shirin auren sun je asibiti an tabbatar da lafiyarsu.


Source: Legit


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN