Allah ya yi wa hamshakin dan kasuwa Alhaji Yahaya Makera rasuwa yau ranar Laraba 1 ga watan Disamba 2021, kuma za a yi jana'izarsa a gidanshi da ke Unguwar Rafin Atiku kusa da ofishin Public complaint commission da karfe 4:30 na yamma yau. Wata majiya da ke da tushe da iyalinsa ya sanar.
Shafin isyaku.com ya samo cewa Alhaji Yahaya Makera ya je gidan Jastis Sadik Usman Muhktar wanda aka fi Sani da Khadi Saddik ne da safiyar Laraba. Yayin da suke tattaunawa da Khadi saddiq sai ya yanke jiki ya jingina a jikin Khadi Saddiq.
Nan take Khadi ya kai shi Asibitin Rabi'at Muhammed Ka'oje inda Dr. Muhammed Sani Ka'oje ya auna shi aka tabbatar da rasuwarsa sakamakon bugun zuciya watau stroke.
Mun samo cewa lafiya kalau Alhaji Yahaya Makera ya bar gidansa kuma lafiaya kalau ake tattaunawa tsakaninsa da Khadi Saddiq kwatsam ya fadi Allah ya karbi ransa.
Za a gudanar da jana'izarsa da karfe 4:30 na yammacin ranar Laraba a gidansa da ke unguwar Rafin Atiku a garin Birnin kebbi, na jihar Kebbi.
Allah ya jikansa ya yi masa rahama.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari