An nada Wildine Aumoithe mai tsawon kafa 2ft da inci 4 a matsayin matar da ta fi kowace mace gajerta a fadin Duniya. Shafin isyaku.com ya samo.
Wildine yar asalin garin Miami ce a jihar Florida na kasar Amurka. A baya bayannan Guinness World Record, ta nada ta mace mafi gajerta a Duniya da bata zirga-zirga.
Wildine yar shekara 18 tana da nau'in gajerta da ba kasafai ake samu ba a cikin al'umma da ake kira SADDAN dysplasia,
A lokacin da aka haife ta, Likitoci sun gaya wa iyayenta cewa ba za ta rayu fiye da awa 24 ba.
Yanzu kam Wildine tana da shekara 18 a wannan shekara, kuma har ta samu nadin matar da ta fi kowace mace gajerta a Duniya.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka