Kungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'a Wa'iƙamatis Sunnah (JIBWIS) wacce aka fi sani da Izala ta bada umarnin fara addu'oin Alkunut a masallatan Ahlissunnanh na faɗin Najeriya.
Shugaban kungiyar na ƙasa, As-sheikh Abdullahi Bala Lau, shine ya bada wannan umarni a wata rubutacciwar takarda da aka raba wa manema labarai.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook, Bala Lau yace wannan umarnin ya shafi masallatan Jumu'a da na kamsus salawat mallakin Izala da na Ahlissunnah dake faÉ—in kasar nan.
Wannan mataki da Izala ta É—auka ya zo ne bayan mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Saad Abubakar, ya bada umarnij yin Alkunut.
A cigaba da addu'o'i a kowane majalisi - Bala Lau
Shugaban Izala yace:
"Dukkan wasu majalisu da ke gudanar da karatun addinin musulunci, da haddan littafi mai tsarki (Alƙur'ani), muna bada umarnin a cigaba da addu'o'i."
"Hakazalika mata dake gida su bi wannan umarni ta hanyar yawaita azkar da kuma fatan Allah ya tausayawa wannan al'umma."
Shehin Malamin yaa kara da cewa matukar mutane suka dage da yin Addu'o'i kuma da kyakkyawar niyya, to Allah zai amsa mana ya magance mana yan ta'adda da masu É—aukar nauyin su.
"idan muka yi wannan da kyakkyawar niyya, muna kyautata zaton Allah amshi rokon mu, ya magance maɓa matsalolin da muke fama da su."
Zamu samu zaman lafiya mai dorewa a yankunan da lamarin yafi ƙamari da izinin Allah mahaliccin kowa."
Yaushe wannan umarni zai fara aiki?
Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa wannan umarni zai fara aiki ne nan take, ba tare da bata wani lokaci ba. Allah ya mana jagora a dukkan harkokin mu na yau da kullum, ya kuma kawo mana dawwamammen zaman lafiya a kasa, inji shi.
Source: Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI