Yan majalisar tarayya sun fara shirin amfani da karfinsu domin tabbatar da kudirin zabe a matsayin doka, amma wannan yunkurin ya wargaje.
Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wasu Gwamnoni sun shiga cikin wannan magana, hakan ya sa adadin kuri’un da Sanatoci suke bukata ya kara yin kasa.
Majiya mai karfi tace gwamnonin APC da na PDP sun kira ‘yan majalisunsu, inda su ka bukaci su ajiye batun warware matakin da shugaban kasa ya dauka
The Nation tace gwamnan jihar Yobe kuma shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ne ya jagoranci gwamnoni wajen rushe shirin ‘yan majalisar.
Sauran gwamnonin da suka lallashi Sanatocin da ke da wannan shiri su ne: Kayode Fayemi, Atiku Bagudu, Yahaya Bello, Gboyega Oyetola da Hope Uzodinma.
Duka gwamnonin ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne kuma su na da ta-cewa a siyasar jihohinsu.
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka