An cafke wasu Mata guda hudu da wani mutum bisa zargin kai wa yan bindiga Karuwai a cikin daji. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Yayin da yake gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin a Shelkwatar yan sanda da ke Abuja,Kakakin hukumar yan sandan Najeriya Frank Mba, ya ce wadanda ake zargin sun hada da Maryam Abubakar, Lawisa Hassan, Jummai Ibrahim da Hajara Abubakar. Shi kuma na mijin sunansa M. Mohammed.
Kazalika Mba ya ce wadan da aka kama suna yi wa wani rikakken dan ta'adda mai suna Isah Ibrahim harkokin leken asiri.
Ya ce za a gurfanar da su a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka