Babban Malamin Addinin Musulunci a Arewacin Najeriya ya fice daga jam'iyar APC, duba dalili


Sheikh Ibrahim Khalil, fittacen malamin addinin Musulunci kuma shugaban majalisar malamai a Kano ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.

Malam Ibrahim Khalil ya sanar da ficewar tasa ce daga APC a daidai lokacin da jam'iyyar ke fama da rikici tsakanin bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Shehin malamin ya shaida wa BBC cewa: "To ni a matsayina na dan jam'iyyar APC kuma daya daga cikin dattawa da kuma daya daga cikin caucus, abin da nake so in tabbatar shi ne na fita daga jam'iyyar APC."

Komai a rayuwa mai dalili ne. Dalilai iri uku ne: ko dai masu ilimi da hankali su sani, ko kuma kowa da kowa su sani, ko kuma mutum shi ya san dalilinsa," in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ya fice ne daga APC saboda wasu na cewa sun sauke shi daga jagorantar majalisar malaman jihar ta Kano, sai ya musanta haka.

"Idan da wannan ne dalilin, da tun lokacin zan sauka. Ba shi ne dalilin ba, domin kamar yadda ban yi bayanin rabuwa ta da gwamnati ba, wannan ma ba sai na bata lokaci na yi bayani a kansa ba."

Ya kuma ce har yanzu yana nan a matsayinsa na dan siyasa.

"Ai ban daina siyasa ba, kuma ban ce ba zan yi jam'iyya ba. Dama shiga ta ANPP ba ni na kai kaina ba, masoya ne suka yi min rajista a jam'iyyar. Don haka yanzu ne zan shiga jam'iyyar da na ga dama da kaina."

Da aka tambaye shi ko zai fito takarar mukamin gwamnan Kano, sai ya ce, "Dama ban taba cewa na daina takara ba domin takara ta jama'a ce, kuma su suka neme ni in yi, sannan ba su ce in daina ba."

BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN