Yan bindiga sun kai farmaki har cikin masallaci da ke garin Tella a karamar hukumar Gassol ta jihar taraba inda suka yi garkuwa da masallata hudu.
Wani mazaunin Tella, Suleiman Rabiu, ya sanar da Daily Trust cewa 'yan bindigan sun kai su 12 da suka zagaye masallacin wurin karfe 7 da minti 12 kuma sun sace masallatan yayin da suke tsaka da sallar Isha'i.
Majiyar ta ce 'yan bindiga sun katse wa jama'a sallar inda suka tasa keyar masallatan da bindiga a kansu.
Daily Trust ta ruwaito cewa , 'yan bindigan daga baya sun saki mutum daya tare da yin awon gaba da sauran zuwa inda babu wanda ya sani.
Daga cikin wadanda aka sace akwai Alhaji Yahaya, Aminu Dali da Alhaji Hussaini, wanda shi ne shugaban masu kasuwanci hatsi na yankin.
Mazaunan yankin Gassol suna fuskantar farmakin 'yan bindiga wadanda ake zargin suna komawa yankin daga jihar Zamfara sakamakon matsanta musu da sojoji suka yi.
Mazaunan yankin Gassol suna fuskantar farmakin 'yan bindiga wadanda ake zargin suna komawa yankin daga jihar Zamfara sakamakon matsanta musu da sojoji suka yi.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da farmakin masallacin amma bai sanar da dalla-dallan yadda lamarin ya faru ba.
Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya.
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka