Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya lashe zaben kananan hukumomi shida kawo yanzu da ake cigaba tattara kuri'un da aka kada.
Kananan hukumomin sun hada da Awka South, Onitsha South, Enugu Anambra East, Anaocha, Anambra East da Njikoka
Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da cewa za'a cigaba da tattara sakamakon zaben ranar Lahadi.
Akwai kananan hukumomi 21 a jihar Anambra amma sakamakon 4 kadai aka sanar a hukumanci.
Kawo yanzu, Charles Soludo na da jimillar kuri'u 47,216 daga kananan hukumomin shida, yayinda dan takaran PDP, Valentine Ozigbo na PDP ke biye da shi da kuri'u 17,952, sannan Andy Uba na APC mai kuri'u 11,361.
Legit Hausa
Rubuta ra ayin ka