Mai martaba Sarkin Argungun, Alhaji Samaila Muhammadu Mera, a ranar Juma'a a jihar Kebbi, ya nada Shugaban Majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin Ganuwan Kabi.
Wannan nadi na cikin bukukuwan cikar Sarkin Argungun shekaru 25 kan karagar mulki, Ola Awoniyi mai magana da yawun Ahmad Lawan ya sanar.
Wadanda aka yiwa nadu kuma a bikin sune tsohon Gwamnan jihar Abia kuma mai tsawatarwa a majalisa, Orji Uzor Kalu(a matsayin Kibiyan Kabi), da kuma Shugaban kamfanin wutan lantarkin Kaduna KEDC, Engr Garba Haruna Argungu.
Wadanda suka halarci bikin sun hada da gwamnonin, Sarakunan gargajiya da kuma yan majalisar dokokin tarayya.
Daga cikin gwamnoni akwai jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni; da Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari.
Daga cikin Sarakunan gargajiya kuwa akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad III; Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero; da Mai martaba Sarkin Zazzau, Amb Bamalli.

Source: Facebook
Sauran sune Sarkin Bade, Sarkin Biu, Sarkin Machina, Sarkin Lafiya, Sarkin Zuru da Sarkin Zamfara.
Cikin yan majalisa kuwa akwai Sanata Barau Jibrin, Sanata Muhammad Musa Bello, Sanata Chukwuka Utazi, Yahaya Abdullahai, Sen. Shuiabu Iau, Sen. Michael Nnanji.

Source: Facebook
Source: Legit Nigeria