Soludo na APGA ya bi yan takaran APC da PDP har garuruwansu ya lallasa su


Dan takaran jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Charles Soludo, ya bi manyan abokan hamayyarsa karamar hukumarsu kuma ya lallasa su.

Charles Soludo ya lallasa Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Aguata.

Daga cikin gundumomi 20 dake karamar hukumar Aguata, Soludi ya kashe Isuofia, Nkpologwu, Igbo-Ukwu I/II, Ekwulobia II, Umuchu I da II, dss, rahoton Premium Times.

He polled a total of 9,136 votes out of the 19,548 valid votes cast.

Ya samu jimillar kuri'u 9,136, yayinda Andy Uba ya samu 4,773 kuma Ozigbo ya samu 3,798.

A cewar baturen zabe karamar hukumar Aguata, Alim Ajake, ba'a yi zabe a wasu rumfunan zabe a gundumomi hudu ba.

Wannan sun hada da Umuchu I (Mutum 2,292), rumfunan biyu a Ekwulobia II, rumfuna uku a Igbo-Ukwu I, da rumfuna biyar a Igbo-Ukwu II

Legit Hausa
Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN