Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe


Duk da akwai 'yan takara 18 tare da jerin jam'iyyun siyasa da suka fito gaba-gadi domin neman kujerar gwamnan jihar Anambra a zaben da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba, akwai 'yan takarar da babu shakka za a fafata da su.

Daga cikin 'yan takarar akwai Fafesa Charles Chukwuma Soludo, wanda shi ne dan takarar jam'iyya mai mulki a jihar ta All Progressives Grand Alliance (APGA).

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe
Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe. Hoto daga Charles Chukwuma Soludo Source: Facebook
Ga wasu manyan dalilai hudu da za su iya sa tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya samu nasarar lashe zaben.

1. Karfin ikon masu madafun iko
Daya daga cikin abubuwan da za su iya saka Soludo ya yi nasarar shi ne, ikon da suke da shi na cewa jam'iyyarsu ke mulki.

A Najeriya da kasashe masu yawa da ke mulkin damokaradiyya a duniya, matukar wanda ke kan madafun iko ko kuma dan takarar jam'iyya mai mulki, ya na da wata dama fiye da sauran 'yan takara.

A sama da shekaru 15, daga Peter Obi zuwa Willie Obiano, APGA ta kasance jam'iyyar da ke mulkin Anambra. Ita kadai ce jihar da jam'iyyar ke mulki a Najeriya.

Duk da zama dan takarar jam'iyya mai mulki bashi da tabbacin cin zabe, ta yuwu gwamnan babban bankin ya lashe zaben.

2. Bayanin martabar Soludo
Daga cikin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar Anambra, martabar Soludo ta zama ta daban. Baya ga shugabantar babban bankin Najeriya, Soludo ya na da wata gogewa a zaman da yayi mai bada shawara kan tattalin arziki ga shugabannin kasa: Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari.

A matsayinsa na Farfesan tattalin arziki, Soludo ya yi aiki a bangarorin kudi daban-daban na duniya.

A matsayinsa na tsohon dan takara kujerar gwamna karkashin jam'iyyar PDP a 2010, Soludo ya na fahimtar siyasar Anambra kuma sanin shi da 'yan jihar suka yi abun dubawa ne.

4. Kokarin da yayi a lokacin fafatawa da sauran 'yan takara
A ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, Soludo da 'yan takarar APC da na PDP sun fafata a wata muhawara da gidan talabijin nna Arise News ta shirya.

Babu shakka Soludo ya zama zakaran gwajin dafi wanda kuma ya tafi da zukatan masu kada kuri'a da yawa a Anambra.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN