Matashi ya ga tsohon Malaminsa ya talauce babu aiki, ya mayar da Miloniya cikin kwana 3


Wani matashi dake fafutukar neman halaliyarsa ya yi kicibis da wani dattijo yana kwana cikin mota a bakin titi Da ya kusanci dattijon sai ya gano cewa tsohon Malaminsa ne wanda ya rasa muhallinsa da aikin sa sakamakon annobar Korona Tsohon dalibin ya taimakawa tsohon Malaminsa kuma ya kama masa Otal kuma ya roki mutane su taimaka masa.

Wani Malami ya shiga halin talauci da kunci bayan rasa aiki da muhallinsa sakamakon annobar Korona da ta bulla a duniya a shekarar 2020. Goal Cast ta ruwaito cewa wani matashi mai suna Steve Nawa ya gano wani dattijo yana kwana cikin mota yayinda yake hanyar tafiya aiki. 

Kawai sai ya kusanci mutumin amma abin mamaki sai ya ga Jose Villaruel, tsohon Malaminsa ne a kasar Amurka. 

 Malaminsa ya talauce gaba daya Steve ya tattauna da Mr Villaruel inda ya fahimci halin da tsohon Malaminsa ke ciki tun bayan annobar Korona. 

Dattijon ya bayyana masa cewa hanya daya tilo da yake samun kudi wani tallafin gwamnati ne kuma matarsa dake rashin lafiya a Mexico yake turawa kudin. 

Steve ya canza rayuwar tsohon Malaminsa Rahoton ya bayyana cewa kai tsaye Steve ya dauke Malaminsa daga kan titi kuma ya kama masa dakin Otal kuma ya bashi kyautan $300 (N123,846). 

A riwayar News Yahoo, dalibin ya garzaya kafar Intanet ya kafa shafin GoFundMe kuma ya samu nasarar mutane suka hadawa tsohon Malaminsa $15,000 (N6,192,300). Bayan gudunmuwan da mutane suka bada, an tarawa mutumin $27,000 (N11,146,140) cikin kwanaki uku. 

Legit Hausa
Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE