Da duminsa: Dan Zuru ya Musulunta a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi, duba dalili (Hotuna)Wani dan Zuru mai suna Danjuma Danlami ya Musulunta a babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi ranar 5 ga watan Nuwamba, kuma ya amsa sunan Musulunci zuwa Muhammad Basharu.

Muhammad ya ce ya dade yana sha'awar shiga Musulunci, amma ya gamu da adawar haka daga iyayensa.

Ya ce yanzu iyayensa sun rasu sakamakon haka ya sami damar idar da sha'awa da aniyarsa ta shiga Addinin Musulunci.

Ya ce ya zo Birnin kebbi ne domin gudanar da aikin hannu a Unguwar Badariya kafin shigarsa Musulunci a yau.


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN