Yanzu yanzu: Wata motar daukar kaya ta fada cikin babbar kwalbati a Birnin kebbi


Wata mota kirar Mazda ta daukar kaya, ta fada cikin babban kwalbati a gefen shataletalen sabon gidan gyara hali, da ke fuskar gidan man NIPCO kan tagwayen hanyoyi na Sani Abacha da ke garin Birnin Kebbi. Shafin isyaku.com ya samo.

Kawo yanzu babu wanda ya tabbatar da hakikanin yadda lamarin ya faru da karfe 7 na safiyar ranar Talata 30 ga watan Nuwamba.

Sai dai wani bawan Allah da ya jiyo karar faduwar motar a cikin kwalbatin domin yana daga daya ketaren titi ya ce.

"Na jiyo karar faduwar motar, sai na rugo tare da wasu jama'a zuwa wajen. Kuma jama'a suka taimaka aka ciro mutanen da ke cikin motar. Shi direba ba abin da ya same shi. Amma yaron mota yana nufashi daya-daya amma yana raye ko da aka wuce da su Asibiti".

Motar ta ci gaba da yin karar oda bayan ta fada cikin kwalbatin. Sai dai wani bawan Allah ya yi kokari ya shiga ya balle wayar kan baturin motar sakamakon haka karar oda ya tsaya.

Allah ya kara kiyayewa ya ba wadanda suka sami rauni lafiya.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN