Shahararren malamin addinin islama, Sheikh Abubakar Giro Argungu, ya bayyana cewa kashi 85 cikin É—ari na yan Najeriya ba su da gaskiya wajen rike amana.
Aminiya Hausa tace Sheikh Giro, ya yi wannan furucin ne a wurin wani taron wa'azi da aka shirya don murnar aure a jihar Nasarawa.
Babban malamin ya yi kira ga yan Najeriya baki É—aya su guji aikata cin hanci da rashawa, kuma su rinka kwatanta adalci da tsare gaskiya a rayuwarsu
Addu'a ce kaɗai mafita a yanzu - Sheikh Argungu Shehin malamin ya bukaci mutanen Najeriya kada su gajiya, su cigaba da addu'a Allah ya kawo karshen ƙalubalen tsaro da yaƙi ci yaƙi cinye wa a ƙasar.
A cewarsa a halin da kasar nan ke ciki yanzun, Addu'a ce kaɗai mafita ɗaya tilo da zata dawo da zaman lafiya da kuma dunƙulewa a Najeriya.
Malamin yace: "Matuƙar muka dage da rokon Allah (SWA), to zai amsa mana ya kawo karshen ta'addancin yan bindiga, kuma ya kawo zaman lafiya da aminci, da kuma cigaban ƙasa."
Malam Abubakar Giro, ya yi wannan kira ne a wurin taron wa'azin aure da ya gudana a Umaisha, karamar hukumar Toto, jihar Nasarawa.
Legit.ng Hausa ta gano cewa an shirya wannan wa'azi ne domin murnar auren mata ta uku da kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya yi.
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI