Da duminsa: Kwastam a jihar Katsina sun kama mota makare da kudi fiye da Naira Miliyan 71 za a fita da su ta jamhuriyar Nijar cikin tsakiyar dare


Rundunar hana fasa kwabri na kasa reshen jihar Katsina Nigeria Customs Service (NCS) ta ce ta kama wata mota makare da Naira Miliyan saba'in da daya da dubu dari biyar da hamsin kudin Najeriya N71,350,000 wanda ake zaton na almundahana ne. Shafin isyaku.com ya samo.

Mukaddashin Kwanturolan na rundunar NCS reshen jihar Katsina, Dalhat Wada-Chedi, ya sanar wa manema labarai ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba yayin da yake bayani kan nassarori da rundunarsa ta samu a jihar Katsina a watan Nuwamba 2021.

Ya ce an kama wasu mutane uku a kauyen Dan Isa wanda ke bakin iyaka da jamhuriyar Nijar cikin tsakiyar dare dauke da kudaden a cikin booth na mota kirar Toyota Corolla mai kalar toka a kan hanyar Jibia zuwa Katsina.

Ya ce sun bayar da ajiyar kudin a babban Bankin Najeriya reshen jihar Katsina domin a ajiye masu kudin daga bisani suka bayar da belin wadanda aka kama.

Ya ce sun sanar da babban Shelkwatar hana fasakwabri na kasa, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE