Yanzu yanzu: Babbar Kotun tarayyar Najeriya ta ayyana Yan bindiga a matsayin "Yan ta'adda"


Wata babbar Kotun tarayya karkashin Mai Sharia Justice Taiwo Taiwo da ke zamanta a Abuja, ta ayyana  Yan Bindiga a matsayin Yan Ta’adda.

Alkalin ya bayar da odan ex parte bayan Gwamnatin tarayya ta gabatar da bukatar haka a gaban Kotun.

Babban jami'i mai gabatar da kara na tarayya a ma'aikatar Sharia na kasa, (DPP) Mohammed Abubakar ne ya gabatar da takardun karar amadadin Gwamnatin tarayya, wanda a ciki Gwamnati ta bukaci Kotu ta ayyana Yan bindigan daji, Kungiyoyin masu aikata miyagun ayyuka a matsayin Yan ta'adda.

A cikin Takardun da aka gabatar a gaban Kotu, wasu Takardun da ke da alaka da harkokin tsaro sun tabbatar da cewa Yan bindigan ne ke da alhakin kashe-kashen bayin Allah, fyade, sace-sacen mutane da sauran ayyukan keta mutunci da haddin bil' adama a yankin arewa maso gabas da arewa maso tsakiyar Najeriya.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN