Type Here to Get Search Results !

Bayan sun yi kaca-kaca tare da matarsa a gida, Maigida ya yi mutuwar gaggawa a cikin dakin wani Otel, duba yadda ta faru


An sami gawar wani mutum mai suna ThankGod a cikin dakin wani Otel a garin Eleparanwo da ke karamar hukumar Obio/Akpor a jihar Rivers. Shafin isyaku.com ya wallafa.

Rahotanni sun ce mutumin ya kama dakin Otel din ne a dare da ya gabata bayan ya sami matsalar iyali tare da matarsa a gida.

Wani ma'aikacin Otel din da ya gan gawar ya shaida wa Jaridar Punch yadda lamarin ya faru. Ya ce mutumin ya fasa gilashin dakin kuma ana zargin cewa ya yi amfani da gilashin ne ya yanke makogoron wuyansa.

Ya ce sun kula cewa lokacin ficewar mutumin daga dakin ya yi kuma basu ji daga wajenshi ba. Sakamakon haka suka je domin su bincika.

Sai dai sun tarar da dakin a kulle daga ciki. Sun balle kofar dakin kuma suka gan halin da yake ciki. Iyalinsa na wajen a lokacin da aka balle kofar dakin Otel kuma a gaban idanunsu aka gudanar da komi.

Kakakin yansandan jihar Nnamdi Omoni, ya ce ya sami labarin aukuwar lamarin. Ya ce sai dai izuwa lokacin bayani bai sami cikakken rahotu daga DPO na garin ba.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies