Yan sanda sun kama ɗan fashi mai suna 'Aljan' a Kano


Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta sanar da kama wani da take zargin riƙaƙƙen ɗan fashi da makami ne mai suna Sabitu Ibrahim wanda ake kira da Aljan da ke a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da kama shi a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya bayyana cewa Aljan na daga cikin mutanen da dama rundunar ƴan sanda ke nema ruwa a jallo kuma bayan an kama shi, an same shi da keke-napep

Bayan binciken da ƴan sandan suka yi, wanda ake zargin ya tabbatar wa ƴan sandan da cewa ya haɗa baki da wasu mutane inda suka kai hari ga wani mai keke-napep a Ɗorayi inda kuma ya shaƙe shi da wayar keble domin kashe shi amma ya tsira da raunuka.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE