Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya ragargaji mayaƙan Boko Haram/ISWAP 26 a Gajiram


Rundunar sojin Operation Haɗin Kai ta samu nasarar hallaka yan ta'addan Boko Haram da ISWAP da yawa a Gajiram jihar Borno Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin sun yi luguden wuta kan yan ta'addan yayin da suka yi yunkurin kai farmaki Hafsan soji, Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin kada su yi ƙasa a guiwa, su tabbata sun kakkabe ragowar yan ta'addan 

Dakarun sojin sama da na ƙasa na rundunar Operation Hadin Kai sun ragargaji yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a wani luguden wuta ta sama. Sojojin sun kaddamar harin bama-bamai kan yan ta'addan a Gajiram, karamar hukumar Nganzai, jihar Borno ranar Lahadi 28 ga watan Nuwamba, 2021. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar soji ta fitar a shafin Facebook ɗauke da sa hannun kakakinta, Onyema Nwachukwu 

Sojojin sun yi luguden wuta kan yan ta'addan yayin da suka yi yunkurin kai farmaki sansanin soji da motocin yaki da wasu manyan makamai. 

Sojoji sun kwato makamai Kakakin sojin ya cigaba da cewa yan ta'addan sun tsere da raunuka a jikinsu kasancewar sojoji sun kashe su da yawa kuma sun lalata kayan aikin su. 

Yace: "Sojojin sun bi sawun yan ta'addan da suka tsere kuma zuwa yanzun sun kwato makamai da suka haɗa da bindigun AK-47 guda 10, bindigidar kakkaɓo jirgi guda ɗaya, Alburusai 62 da sauran su." "Haka nan kuma an gano ƙonannun gawarwakin yan ta'addan a kan hanyar da suka bi. Amma abin takaicin shine sojoji biyu sun kwanta dama yayin gwabzawar." 

COAS ya yaba wa sojojin Shugaban rundunar sojojin ƙasa, Janar Farouk Yahaya, ya roki dakarun sojin kada su gajiya su cigaba da matsawa ragowar yan ta'adda lamba har sai sun kawo karshen su. 

Legit News

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN