Fitattun taurari sun bayyana yadda ake cin zarafin mata a Nollywood da masana'antar waka


A baya- baya nan ne wasu shahararrun 'yan Najeriya suka bayyana yadda suke fuskantar matsala saboda jinsi wajan gudanar da harkokinsu.

Wannan na zuwa ne bayan da fitacciyar mawakiya Simi wadda ta lashe lambar yabo ta jagoranci wani gangami a shafin Instagram a kan wariyar da ake nuna wa mata mai taken #NobodyLikeWoman.

Ya ba da wuri mai aminci ga taurari da sauran mata domin bayyana matsalar wariya da suka rika fuskanta.

Sun kasance suna saka hotunan bak'i da farare sannan suna zazzage su da kalaman sukansu, kamar: "Uwa ce, ta zauna a gida", "Me ya sa ta fita da dare idan ba karuwa ba? " kuma "Me ya sa har yanzu ba ki yi aure ba?"

Simi ta shaida wa BBC cewa ta yi kuka yayin da ta karanta wasu daga cikin sakonnin da aka tura mata a shafukan sada zumunta.

Sako ne a kan wata mace da aka yi wa izgili saboda an yi mata aikin tiyata sau hudu a duk lokacin da take dauke da juna biyu.

Mutane sun tambayi dalilin da ya sa ba za ta iya haihuwa ba.

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

Ta ce kalaman sun yi tsauri: " Sai da aka yi mata aikin tiyata kuma sai da ta rasa daya daga cikin 'yayanta ." Wannan yana da ban tausayi sosai."

Mawakiyar mai shekaru 33 ta ce ta fara gangamin ne domin mata su fahimci cewa ba su kadai ba ne a gwagwarmayar da suke yi kuma gangamin ya zo ne a dai-dai lokacin da ta saki sabuwar wakar ta mai suna Mace.

Sai dai yawan matan da suka yi amfani da shafin domin bayyana yadda ake nuna mu su wariyar jinsi a rayuwarsu da wurin aiki ya kasance abin mamaki.

Wani hoton Simi da ke dauke da rubutun da ke cewa : "Yaya za ta nemi irin wannan kudin, ba tana da juna biyu ba ?" wanda aka rubuta a bayanta shi ne ya ja hankalin mutane.

A matsayinta na shahararriyar mawakiya a Afrika da sauran kasashe , Simi ta ce ta ce hoton ya fito da masalar wariyar jinsi da ta rika fuskanta a masana'antar waka ta Afro beat.

A lokacin da ta fara waka, shugabannin kamfanonin waka wadanda galibinsu maza ne sun fada mata cewa dole ta kasance wadda za ta rika jan hakalin maza ta hanyar saka tufafi marasa mutunci domin ta yi nasara a harkar waka. Sai dai ta yi watsi da su.

Lokacin da tauraruwarta ta haskaka, sun yi mamaki.

Akwai ma wadanda ba sa son yin aiki da mata, saboda suna ganin ba za su iya yin aiki ba bayan sun haihu ko kuma sun yi aure, in ji ta.

A wani al'amari ta yi magana a kan yadda wani ya tambayi dalilin da ya sa ta ke tsawwala kudi a tikitin kallon wasan wakarta yayin da take da juna biyu.

"Wataƙila wata cibiya ce," in ji ta, lokacin da aka tambaye ta ko wanene ya yi mata wannan tambayar.

'Idan kina son ki zama jaruma to dole ki kwana da ni'

Ita ma jarumar Nollywood Chioma Omeruah da aka fi sani da Chigul ta ce ta sha fama da irin wannan gwagwarnaya kuma ta yi ammanar cewa matsalar al.'ada ce

"A al'adance mu ba ma sus on su yi magana ba ne," in ji jarumar mai shekaru 45 da haihuwa.

A lokacin da ta ke harkar fim, Chigul ta ce mata da dama 'yan fim sun yi zargin cewa shugabanninsu maza sun yi kokarin lalata da su.

Wasu daga cikinsu mazan darektoci sun ce: "Ki zo ki kwana tare da ni, zan sa ki zama tauraruwa.

Chigul da Simi dai sun yarda cewa ya kamata a samu dokoki masu tsauri a Najeriya a kan masu nuna wariya ko cin zarafi ta hanyar lalata.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya Mata, Najeriya ta aiwatar da kashi 75 cikin 100 na dokokin da ake bukata domin inganta daidaiton jinsi - wanda Majalisar Dinkin Duniya ke son cimmawa a duniya nan da shekarar 2030.

Sai dai kasa da rabin matakan da ake bukata don sa ido kan ci gaban kasar kan wannan buri aka aiwatar a bara - misali tarin kididdiga na yau da kullun kan abubuwa kamar gibin albashin tsakanin maza da mata da cin za

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN