Ya sayar da jaririn matarsa kan N350.000 ya ce Jariri ya mutu, duba dali da ya sa asiri ya tonu (Bidiyo)


Rundunar yan sandan jihar Abia ta kama wani mutum mai suna Appolos Ndubuisi mai shekara 40, tare da wata mata mai suna Rose Godwin Chinweikpe yar shekara 66 bisa zargin sayar da jaririn wata mata mai suna Deborah Onukaogu yar shekara 24, wacce suke zaman dadiro tare da Appolos Ndubuisi. Shafin isyaku.com ya samo.

Kwamishinan Yan sandan jihar Abia CP Janet Agbede, ta sanar wa manema labarai . Ta ce Deborah Onukaogu da ke zaman dadiro da Appolos Ndubuisi, ta dauki ciki ba tare da an daura masu aure ba. Shi dai Appolos dan kauyen Umuariaga ne a karamar hukumar Ikwuano da ke jihar Abia. 

Shafin isyaku.com ya labarta cewa Kwamishina Onukaogu ta ce daga nan sai Appolos Ndubuisi ya kai Onukaogu zuwa gidan wata Unguwar zoma da bata da lasisi a garin Owo-Ahia-afor da ke karamar hukumr Obingwa, mallakin wata mata mai suna Rose Godwin Chinweikpe wanda aka kama su tare. 

Sai suka hada baki suka sayar da jaririn da Onukaogu ta haifa ranar 26 ga watan Yuni 2020 a kan N350.000. Daga bisani suka gaya mata cewa jaririn ya mutu lokacin da take nakuda.

Sakamakon haka Onukaogu ta dangana. Sai dai balli ya tashi ne bayan Appolos ya sake dirka wa Onukaonu cikin babu aure, ta nemi shi mafita a kan zancen cikin. Sai Appolos ya gaya mata cewa zai kai ta wajen da ta haifi Jariri na farko a 2020 domin idan ta haihu sai su sayar da jaririn.

Wannan lamari ya haifar da zargi tare da tuhuma mai karfikarfi daga wajen Onikaogu, sakamakon haka ta kai kara wajen Yan sanda. Lamari da ya haifar da tonon silili kan ainihin yadda aka yi da jaririnta da ta haifa da farko. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN