Da duminsa: Wata gawa ta tashi a Mutuware lokacin da dalibai suka je domin daukar darasin ilimin jikin dan Adam, dalibai sun gudu (Bidiyo)


Wata gawa da aka ajiye a dakin ajiye gawa na Jami'ar koyon aikin Likita na jihar Edo da ke Benin ta tashi lokacin da daliban anatomy ilimin jikin mutum suke kokarin daukan darasi ta hanyar yin amfani da gawar. Shafin Isyaku.com ya tattaro.

.

Wani ganau ya ce iyalin gawar wanda wata Mata ce ta mutu, sun kammala cika takardun da suka wajaba sai suka ajiye gawarta a dakin ajiye gawa, Mutuware (Mortuary) sai suka tafi. 

Shafin isyaku.com ya samo cewa daliban masu koyon aikin Likita kan ilimin jikin mutum da suka je domin daukar darasi ta hanyar yin amfani da gawar, sun shiga dakin ajiye gawar domin a fara daukan darasi. Kwatsam sai gawar ta tashi. Nan take dalibai suka watse da gudu suka yi rige-rige wajen ficewa daga dakin ajiye gawa. 

Sai dai daga bisani sun dawo suka taimaka wa gawar suka kai ta waje cike da mamaki suka kai ta wajen wata mota da ke waje.

An gan wasu daga cikin daliban a harabar mutuwaren watau dakin ajiye gawa suna bayyana mamaki kan lamarin, yayin da matar ta kai kanta har wajen motar da kafafunta. 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN