Wani saurayi ya janyo cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ya bayyana irin soyayyar da yake yi wa fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Hadiza Muhammad wacce aka fi sani da Hadizan Saima.
Saurayin mai suna Farouq Abdullahi Tukuntawa ya aike da sakon soyayya zuwa ga jarumar a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa ya gagara cin abinci saboda begenta.
Tukuntawa ya kuma roke ta da ta taimaka ta ceto rayuwar shi daga kogin soyayyar da ya dade da fadawa ciki.
Ga wani bangare na sakon da ya rubuta a shafin nasa:
Hajiya hadiza hakika na Dade ina rokon Allah madaukakin Sarki ya nuna min kwatankwachin wannan rana kafin na koma gareshi
"Ranar da zan furta miki abun da ya Dade azuciya ta koda zaki dauki hakan a matsayin shirme, zan yi farinciki da hakan domin nasan nayiwa zuciya ta babban gata domin na fitar mata da ciwon da ya Dade yana dawainiya da ita."
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI