Kwalejin fasaha ta jihar Osun ta bukaci a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar É—aya daga cikin É—alibanta mata mai suna Wumi.
Jaridar Punch tace É—alibar, wacce take shekarar karatunta ta É—aya a sashin koyon aikin jarida, ta mutu ne ranar Asabar, bayan gajeriyar rashin lafiya a É—akin Saurayinta.
Rahotanmi sun bayyana cewa Wumi na fara nuna wasu alamu na rashin lafiya aka gaggauta kai ta asibiti mai zaman kansa a Iree, amma suka ƙi amsarta.
Ɗalibar ta ƙarisa mutuwa ne yayin da ake kokarin canza mata wani Asibitin na daban.
Shin ana zargin saurayin nata?
Wata ɗaliba da suke karatun kwas ɗaya, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa jami'ai sun damƙe saurayin da zargin hannu a mutuwarta. Ɗalibar tace:
"Wumi ta ziyarci gidan saurayinta a yankin Igaa dake Iree, ba zato sai ta fara fitar da kumfa daga bakinta. Nan take akai gaggawar kaita Asibiti a Iree, amma suka ƙi amsarta, kafin a kaita wani kuma ta mutu."
"Ƙawayenta suka kai rahoto wurin yan sanda, nan take suka turo jami'ai, suka ɗauki gawarta zuwa ɗakin aje gawarwaki a Ikirun."
"Saurayin na ta shima É—alibi ne a kwalejin, jami'an yan sanda sun damke shi, sun tafi da shi ofishin su.
Kwalejin ta tabbatar da mutuwar Wumi Kakakin kwalejin, Tope Abiola, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya bayyana cewa wanda ake zargi ba É—alibin su bane.
Yace: "Eh, dagaske ne É—alibar ND 1 dake karatu a sashin jarida ta rasa rasuwarta, amma ba mu san musabbabin mutuwarta ba."
"Yan sanda na cigaba da bincike. Makaranta na yiwa iyayen É—alibar ta'aziyyar mutuwarta, da zafi sosai matashiyar yarinya ta mutu ba zato ba tsammani."
Source: Legit.ng
Rubuta ra ayin ka