Farashin man fetur zai tashi kwanan nan, kungiyar yan kasuwan mai ta yi gargadi


Kungiyar yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya IPMAN, ta gargadi gwamnatin tarayya cewa da yiwuwan farashin man fetur ya tashi kwanan nan.

Kungiyar tace hakan zai faru ne saboda masu defot sun kara farashi daga wajensu. Shugaban IPMAN na reshen Kano, Alhaji Bashir Danmallam, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, rahoton Punch. Ya ce wasu mammalakan defot masu zaman kansu sun kara farashin man daga N148 ga Lita zuwa N153-N155 tun Juma'ar da ta gabata. 

Yace kungiyarsu na sanar da gwamnati ne saboda kada a daurawa mambobinta laifi idan suka kara farashin mai saboda ba zasu yarda da asara ba. 

Yace: 

Defot masu zaman kansu na kokarin yiwa gwamnatin tarayya zagon kasa ta hanyar kara farashi duk da cewa gwamnati bata daga farashin litan mai ba." 

"Hakazalika muna kira ga shugabannin NNPC suyi bincike kan lamarin saboda masu defot sun kara farashi daga N148 zuwa N153-N155 tun ranar Juma'ar da ta gabata." "Mun san gwamnatin tarayya kadai ke da hakkin shigo da mai Najeriya." 

Ya kara da cewa "yanzu haka, defot dake Warri, Calabar, Legas, da Ogahra a Delta sun kara farashinsu. Muna sa ran NNPC zata yi bincike kan hakan." Ya tuhumci masu defot din da kokarin haddasa tsadar mai saboda suna ganin karshen shekara ya kusa don su samu dimbin riba. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN