Shin bishiyoyi suna yin tunani kamar dan adam?
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Dr. Estrella Luna-Diez daga Jami'ar Birmingham tana jagorantar wani bincike domin gano ko bishiyoyi za su iya tuna wahalar da fari ko raɓa suka haddasa musu.
Binciken wanda kungiyar MEMBRA da ke Birtaniya take gudanarwa ya yi nazari kan samfur-samfur na iri domin ganin ko bishiyoyi za su iya gadar wa 'ya'yansu irin gajiyar da suke fama da ita, da kuma ko 'ya'yan nasu za su jure wa irin wannan gajiya.
BBC Hausa
Rubuta ra ayin ka