Mun fara tattaunawa da Bankin Duniya domin karbo sabon Bashi, Shugaba Buhari


Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara tattaunawa da bankin Duniya kan yadda zata sami rancen dala miliyan $30m.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban yace gwamnatin zata karbo waɗan nan kuɗaɗen ne domin gida ma'aikatar da zata samar da rigakafi a Najeriya.

Buhari ya kara da cewa za'a fara aikin ginama'aikatar sarrafa rigakafin da za'a gina bisa haɗin guiwar kamfanin May & Baker Nigeria Plc shekara mai zuwa.

Mun fara tattaunawa da bankin duniya domin ciwo sabon bashin gida masarrafan rigakafi, Shugaba Buhari Hoto: Professor Yemi Osinbajo Source: Facebook

Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya faɗi haka ne a wurin yaye manyan jami'ai 43 a Jos, jihar Filato, ranar Asabar.

Taron ya samu halartar gwamnan Filato, Simon Lalong, Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Saad Abubakar III, da sauran manyan mutane.

Shirin FG kan sabon bashin

Da yake jawabi ta bakin Osinbajo, Shugaba Buhari yace:

"Najeriya ta fara tattaunawa da Bankin Duniya, domin tara dala miliyan $30m, waɗan za'ai amfani da su wajen gina ma'aikatar sarrafa rigakafin COVID19."

"Kuma za'a fara aikin ginin gadan-gaban a watanni ukun farko na shekara mai shigo wa 2022."

"Wannan ma'aikatar zata cike mana gurbi kuma ta kawo karshen shigo da ɗanyun kayayyakin rigakafi da yi masa mazubi domin rarrabawa."

Shugaban ƙasan ya kara da bayyana cewa nan gaba za'a cigaba da sarrafa rigakafin baki ɗaya a Najeriya.

Bugu da kari yace gwamnatinsa zata kawo karshen karya tattalin arzikin da annobar COVID19 ta yi wa Najeriya ta yadda ba'a tsammani.

Kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da kuma yaɗa labarai na hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Mamoh, yace bana yan Najeriya zasu samu damar sauke farali a kasa mai tsarki.

Prince Mamoh ya bayyyana cewa babu tantama suna da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata zasu gudanar da Hajji.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN