Matasa mu farka mu guji bangar siyasa, don gobenmu tayi kyau - Rukaiya Ajimi Gudumbali

Daga Ƙungiyar "Arewa Media Writers"


Ƙungiyar marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, na kira ga matasa dasu sani sune manyan gobe, kuma sune shugabannin gobe.


Abin takaici a yau irin sunayen da ake kiran matasan mu dasu sune irin:-

'Yan jagaliya
'Yan sara suka
'Yan daba
'Yan shara
'Yan kalare
Ecomog

A dai dai wannan lokaci da muke ciki ya kamata wasu daga cikin ƴan uwanmu matasa su farka, daga wannan hanyar da suke kai, na bangar siyasa kamata yayi musa kishin kai da na ƙasarmu baki ɗaya, sannan mu tashi mu nemi illimi da sana'a sai rayuwar mu ta inganta har mu iya inganta rayuwar al'ummar da muke rayuwa a cikinta.

A yau matasan mu sun mayar da shaye-shaye ɗabi'a, ta yaya wanda baya cikin hayyacin sa zai samu damar inganta rayuwar sa balle har ya gyara ta wani?

Duk uban kirki bazai so yaga ɗanshi yana yawon gara-ramba a kan titi yana shan miyagun kwayoyi ba, dan haka ya kamata suma iyaye su tashi dan kawo karshen wadannan abubuwa, idan kowa ya killace ɗansa tare da hanashi shiga abubuwa marasa kyau tabbas za'a samu gyara tare da kawo sauyi mai kyau.

"Arewa Media Writers" tana kira ga al-umma dasu fahimci muhimmancin zaman lafiya, su hana yaransu shiga bangar siyasa, mu taru mu wayar da kan matasa da nuna musu illar bangar siyasa.

Lallai sai mun nuna da gaske muke sannan Allah zai dube mu ya kawo mana tallafi.

Fatan mu Allah ya zaunar da ƙasar mu lafiya ya shirya matasan mu ya inganta rayuwar su, Allah ya kawo mana karshen matsalolin tsaro da suka addabi yankinmu na Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya.Amin

Rubutawa 
Rukaiya Ajimi Gudumbali,
Daya daga cikin membobin kungiyar "Arewa Media Writers" reshen jihar Borno.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN