Da yawa daga cikin shugabanninmu basu damu da halin damu talakawan kasar muke ciki ba.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Kasarmu ta Najeriya tana fama da Matsaloli masu dumbin yawa da suka hada da; Rashin Tsaro, Cin Hanci da Rashawa, Hassada, Kyashi, Mugunta, Munafurci, Kabilanci, Son Zuciya, Kwadayi, Jahilan 'Yan Siyasa, 'Yan Zaman Banza da sauransu.
Wa 'yan nan sune manya manyan matsalolin da muke fama dasu a Najeriya musammanma yankinmu na Arewa, son zuciyarmu da rashin tsoron Allah yasa muke fama da dukkannin matsalolin.
Da shugabanninmu na Addinai da na 'yan Siyasa, sarakuna, 'yan kasuwa da jagororinmu na kowanne bangare, damu kanmu Talakawan kasar zamu cire Son Zuciya, Hassada, Kabilanci, Munafurci, Mugunta kowa ya koma ga Allah, da kasarmu ta zauna lafiya.
Yau a Najeriya duk wasu shugabanninmu na Addinai da na 'yan Siyasa, sarakuna, 'yan kasuwa da jagororinmu duk sun mance da irin halin kunci da rashin tsaro damu Talakawan kasar muke ciki, sai 'yan kadan daga cikinsu suka damu damu.
Matukar bamu gyara halayenmu ba, kasarmu ta Najeriya ba zata taba jaruwa ba. dole sai mun tsarkake zuciyoyinmu mun koma ga Ubangiji.