Lalurar cutar ciwon siga, abin da ke janyo shi da yadda za ku kare kan ku


Ciwon siga cuta ce ta mutu-ka-raba da ke kashe fiye da mutane miliyan ɗaya a kowace shekara kuma kowa zai iya kamuwa da ita.

Abin da ke haifar da ciwon shi ne idan jiki ya kasa sarrafa duka siga (sinadarin glucose) da ke cikin jini; hakan na iya haifar da bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki da makanta da ciwon ƙoda da kuma guntile gaɓɓai.

Kuma matsala ce da ke ci gaba da ƙaruwa- ƙiyasin mutane miliyan 422 suna fama da ciwon siga a faɗin duniya-ninki huɗu a kan yadda yake shekaru 40 da suka gabata, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO)

Duk da hatsarinsa, rabin mutanen da ke ɗauke da ciwon siga ba su san suna da shi ba.

Amma sauya yadda mutum ke gudanar da rayuwarsa zai iya hana kamuwa da ciwon ta hanyoyi da dama. Ga yadda za a yi:

Mene ne ke haifar da kamuwa da ciwon siga?

Idan muka ci abinci,jikinmu na sarrafa sinadarin carbohydrate ya koma sukari (sinadarin glucose) Wani sinadari da ake kira insulin,wanda ake samarwa a cikin saifa, yana umurtar ƙwayoyin halittar jikinmu su tsotse waɗannan sukarin domin samun ƙarfi.

Ciwon siga na faruwa ne idan ba a iya samar da sinadarin insulin ko kuma ba ya aiki yadda ya kamata, ya janyo sukari ya taru a cikin jininmu.

Sugar cubes and a spoonful of sugar

Bayanan hoto, Ciwon siga na faruwa ne idan ba a iya samar da sinadarin insulin ko kuma ba ya aiki yadda ya kamata

Yaya nau'o'in ciwon siga suke?

Akwai nau'o'in ciwon siga da dama.

A ciwon siga a matakin farko (type 1) saifa tana daina samar da sinadarin insulin, daga nan sai glucose ya yi yawa a cikin jini.

Masana kimiyya ba su da tabbacin takamamammen dalilin faruwar hakan, amma sun yi imani wataƙila hakan ya tasirantu ne da ƙwayoyin halittar gado ko kuma sakamakon bincike a kan ƙwayoyin cuta da ke lalata ƙwayoyin halittar dake samar da sinadarin insulin a cikin saifa. Kimanin kashi goma na adadin mutanen da ke da ke ɗauke da ciwon siga suna da nau'in type 1 ne.

A ciwon siga nau'in type 2, saifa ba ta samar da isasshen sinadarin insulin ko kuma masarrrafi na sinadarin hormone ba ya aiki yadda ya kamata.

Medical illustration of the pancreas

Bayanan hoto, A ciwon siga nau'in type 2, saifa ba ta samar da isasshen sinadarin insulin ko kuma masarrrafi na sinadarin hormone ba ya aiki yadda ya kamata.

Wannan yakan faru ne da mutane masu matsakaicin shekaru da waɗanda suka manyanta, sannan da mutane masu ƙiba da masu yawan zama,da kuma mutane ɗaiɗaiku daga wasu jinsi, musamman na kudancin Asiya.

Za a iya samun wasu matan masu ɗauke da juna biyu da ciwon siga idan jikinsu ya kasa samar da isasshen sinadarin insulin ga su da kuma abin da suke ɗauke da shi.

Bincike daban-daban da aka gudanar tare da yin amfani da dabaru mabanbanta sun yi ƙiyasin cewa kashi shida zuwa Goma sha shida na mata masu ciki suna kamuwa da ciwon siga. Akwai buƙatar su kula da adadin siga da ke jininsu ta hanyar abincin da suke ci da motsa jiki da ko kuma sarrafa sinadarin insulin ta yadda za a hana shi rikiɗa ya zama nau'in type 2.

Har wa yau, za a iya samun mutane da ke daf da kamuwa da ciwon siga-idan aka samu hauhawar sinadarin glucose a jini kuma zai iya kai wa ga samar da cikakken ciwon siga.

Wadanne ne alamomin ciwon siga?

Alamomin da aka fi sani sun haɗa da:

A cewar Hukumar kiwon Lafiya ta Burtaniya, alamomin ciwon siga nau'in type 1 sun fi bayyana tun a ƙuruciya kuma sun fi tsanani.

Mutanen da suka fi hatsarin kamuwa da ciwon siga nau'in type 2 sune waɗanda suka haura shekaru arba'in da haihuwa (ko shekara 25 ga mutanen Asiya ta kudu); da mutum da ke iyaye ko ƴan uwa, uwa ɗaya uba ɗaya masu ɗauke da ciwon siga, da masu ƙiba ko masu ƙibar da ta wuce kima da kuma mutanen ke da tsatson yankin Kudancin Asiya da ƴan ƙasar Sin da ƴan yankin Afrika ko na Caribbean ko ma baƙar fata ɗan asalin Afrika.

Zan iya kaucewa kamuwa da ciwon siga?

Kamuwa da Ciwon siga ya danganta ne da ƙwayoyin gado da kuma wasu abubuwa masu nasaba da muhalli, amma za ka taimaka ka kula da yawan siga da ke shiga cikin jininka ta hanyar cin abinci mai gina jiki da kuma gudanar da rayuwar da ba ganganci a cikin ta.

Bayanan hoto, Kaucewa abinci gwangwani da kayan ƙwalama da lemon zaƙi da komawa cin abinci dangin alkama a maimakon cin na fulawa

Kaucewa abinci gwangwani da kayan ƙwalama da lemon zaƙi da komawa cin abinci dangin alkama a maimakon cin na fulawa da taliya wani matakin farko ne mai kyau.

Sukari da hatsi da aka sarrafa suna da ƙarancin abubuwa masu gina jiki saboda an raba su da ɓangarorinsu masu amfani. Misali sun haɗa da burodin fulawa da shinkafa da taliya da danginta da kayan zaƙi da alawa da kayan karin kumallo da ake ƙara musu sukari.

Abinci mara lahani ya ƙunshi kayan ganye da ƴaƴan itatuwa da wake da kuma dangin alkama. Har wa yau,ya ƙunshi duk dangin mai marasa lahani da kifin gwangwani da danginsa.

Yana da muhimmanci a dinga cin abinci lokaci bayan lokaci kuma ka dakata da cin abinci idan ka ƙoshi.

Shi ma motsa jiki zai taimaka wajen rage yawan siga da ke cikin jininka. Hukumar Lafiya ta Burtaniya (NHS) ta bayar da shawarar a dinga motsa jiki na tsawon awa biyu da rabi a mako ɗaya, wanda ya haɗa da sassarfa da hawa matattakala.

Yana kuma da muhimmanci kar ka sha taba sannan ka kula da yawan kitsen da ke jininka domin rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya.

Kiba mara yawa za ta sauƙaƙa wa jininka ya rage siga da ke cikin jininka. Idan kana bukatar rage ƙiba, ka yi ƙoƙarin yin hakan a hankali, tsakanin kilogiram 0.5 da kilogiram 1 a mako ɗaya.

Yana kuma da muhimmanci kar ka sha taba sannan ka kula da yawan kitsen da ke jininka domin rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya.

Mene ne hatsarin ciwon siga?

Yawan siga a cikin jini zai iya yin mummunan lahani ga jijiyoyin jini.

Idan jini ba ya gudana yadda ya kamata a cikin jikinka, ba zai kai ga sassan jikin da ke buƙatar shi ba, abin da zai ƙara hatsarin jijiyoyi su samu lahani (rasa jin abu ya taɓa ka da kuma jin zafi) da rasa gani da kuma ciwon ƙafa.

WHO ta ce ciwon siga shi ne babban abin da ke haddasa makanta da ciwon ƙoda da bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki da kuma guntile gaɓɓai.

A shekarar 1980, ƙasa da kashi 5% na baligai ( ƴan sama da shekaru 18) suna fama da ciwon siga a faɗin duniya

A shekarar 2016, an yi ƙiyasin cewa ,ciwon siga ne kai tsaye ya yi sanadiyar mutuwar mutane miliyan 1.6.

Mutane nawa ne suke fama da ciwon siga?

A cewar WHO, adadin mutanen da ke fama da ciwon siga ya ƙaru daga miliyan 108 a shekarar 1980 zuwa miliyan 422 a 2018.

A shekarar 1980 , ƙasa da kashi 5% na baligai ( ƴan sama da shekaru 18) suna fama da ciwon siga a faɗin duniya - a shekarar 2014 adadin ya kai kashi 8.5%.

Hukumar kula da ciwon siga ta duniya ta yi ƙiyasin cewa kashi 80% na baligai masu ɗauke da ciwon suna ƙasashe masu tasowa da kuma matalautan ƙasashe ne,inda yanayin cin abinci ke sauyawa cikin hanzari.

A ƙasashe masu arziki,ana alaƙanta shi da talauci da kuma cin abincin gwangwani masu araha.

Rahotun BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN