Type Here to Get Search Results !

Tirkashi: Wani Dalibin jami'a ya lakadawa lakcara mace dukan kawo wuka daga neman taimako


Wani É—alibi dake karantar kwas É—in Microbiology a jami'at Ilorin, (UniLorin) ya lakaÉ—awa lakcaransa dukan kawo wuka. Dailytrust tace ÆŠalibin mai suna, Captain Walz, bai samu yin kwas É—in neman sani makamar aiki ba (SIWES), dan haka yaje neman taimakon lakcaran. 

Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran da abin ya shafa, Mrs Zakaria, ita ce zata kula da É—alibin yayin da zai yi Project a 400 level. 

Hakanan kuma an tabbatar da cewa Walz ya lakadawa malamar tasa dukan tsiya ne ranar Alhamis din nan da ta gabata. 

Meyasa abin ya kai da duka? A binciken da muka yi, dalibin ya je har ofishin malamar domin neman ta taimaka masa, saboda bai samu damar yin SIWES ba kwata-kwata. 

Amma da lakcaran da nuna Æ™in amincewar ta, nan take Walz ya fusata, ya lakaÉ—awa malamar dukan tsiya wanda yasa ta ji raunuka a jikinta. Bugu da Æ™ari, ba'a É—auki dogon lokaci aka kawo mata É—auki kuma aka garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta. 

Wane mataki jami'a ta É—auka? Daraktan hulÉ—a da jama'a na jami'ar, Mr Kunle Akogun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar salula ranar Asabar da daddare. 

Yace: "Eh tabbas lamarin ya auku, amma lakcaran tana yanayi mai kyau, kuma tuni mataimakin shugaban jami'ar (VC). Farfesa Abdulkareem Age da wasu malaman jami'a suka ziyarci lakacaran da lamarin ya shafa." 

"Jami'a baki É—aya bata ji daÉ—in abinda ya faru ba, kumazata tabbatar da an yi adalci. Sannan kuma ya roki a kula da lafiyar malamar yadda ya dace ta asusun jami'a." 

Source: Legit 

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies