Abin mamaki: Duba Amarya yar shekara 55 da ta yi aure bata taba saduwa da namiji ba - Inji Amaryar


A wata hira da tayi da jaridar Punch, Esther ta bayyana cewar duk da dadewar da tayi ba tare da aure ba, ta yi kokarin ganin ta kare mutuncinta, domin a cewarta bata taba sanin 'da namiji ba kafin aurenta. Ta ce ita budurwa ce sabuwa fil a leda.

Ta kuma bayyana cewa bata taba yin soyayya ba har zuwa aurenta, domin a cewarta a lokacin da ta shirya ma aure sai ya zamana babu wani namiji da ya tunkareta da sunan hakan.

Ta ce:

"Shaidan ya so hana ni yin aure. A lokacin da nake ganin na shirya, babu wani namiji da ya zo. Ina ta jiran Allah ya yi ikonsa har sai da na kai shekaru 55. Ban taba soyayya da wani ba har nayi aure. Da farko, na zata matsalar daga tsohon cocina ne sai na bar cocin, amma ina mika godiya ga Allah. Ya cika mun burina a sabon cocina kuma duk wani shamaki ya kau."

Game da ko ta taba yin soyayya da bai kai ga aure ba, matar ta ce:

"A'a, ban taba soyayya ba a baya kafin nayi aure. Na yi rayuwa mai tsafta a zamanin da nake makaranta. Ban taba kowani soyayya ba. Na karbi Yesu da wuri a rayuwa kuma a lokacin da nake a matsayin daliba, ban ma taba tunanin hakan ba, domin na san ban shirya ba a lokacin."

Ta bayyana cewa ta hadu da angon nata ne a wani taro da aka yi a Ilesa, inda tace Allah ne ya tsara komai da komai.

Esther ta kuma bayyana cewa da haduwarsu da kulla auren duk ya zo ne a dan kankanin lokaci. Sannan ta nuna godiya ga Allah da ya tuna da ita bayan lokaci mai tsawo.

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN