Type Here to Get Search Results !

Ku biya mu kudinmu,Masu kada kuri'a sun bi wakilan jam'iyya don karbar cin hanci


Daya daga cikin babbar matsalar da ke cigaba da haifar da matsala a Najeriya shi ne siyan kuri'a, wanda kuma ya cika a zaben gwamnan jihar Anambra.

Wakilan jam'iyyun siyasa da ke kare ra'ayoyin jam'iyuunsu an zargesu da bai wa masu kada kuri'a kudi daga dari biyar har zuwa dubu goma.

Kamar yadda Premium Times ta wallafa, an ga wani wakilin jam'iyya na ganawa da masu kada kuri'a bayan saka kuri'unsu tare da rubuta sunayensu a wata takarda, alamu da ke nuna za a biya su daga baya.

Amma kuma, masu kada kuri'a da ke biye da shi sun ta ihun a biya su hakkinsu a take.

Wannan al'amarin ne ya faru a kusan dukkan rumfunan zabe kamar yadda majiyoyi da ke lura da zaben suka tabbatar.

Jaridar Sahara Reporters ta yi ikirarin cewa, wasu daga cikin wakilan jam'iyyu sun biya dubu goma inda wasu suka biya har dubu shida kan kuri'a daya.

Duk da babu takamaiman jam'iyyar da suka siya kuri'a, an gano cewa kusan dukkan jam'iyyun siyasan ne suka dinga siyen kuri'un.

Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya isa rumfar zabensa da wuri amma ya kasa saka kuri'arsa saboda rashin aikin na'urar BVAS a wurin.

Dan takarar APGA din ya ce zai zanta da manema labarai bayan ya kada kuri'arsa cike da nasarar. Kamar yadda rahoto ya bayyana, a lokacin, mutum tara kacal ne daga cikin sama da dari bakwai suka saka kuri'arsu a rumfar zaben.

Source: Legit

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies