Yadda aka riƙa cinikin ƙuri'a a zaben Anambra


Zaɓen gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ya gabata a ranar Asabar, sai dai wani sabon abu da ya fito fili shi ne yadda aka rinƙa sayen kuri'ar masu zaɓe a fadin jihar yayin wannan zaɓe.

Wani mai sanya ido na hukumar zaɓen Najeriyar wato INEC ya shaida wa BBC cewa ya ga wakilan jam'iyyu daban-daban a rumfunan zaɓe na siyan kuri'ar jama'a a wasu yankunan jihar, da suka haɗar da karamar hukumar Dunukofia, da Anaocha, da Awka, da Njikoka da Aguata.

Jami'in ya ce ''Jama'a kin fitowa suka yi sai wajen ƙarfe huɗu na yamma, saboda an fara fito da kuɗi, an fitar da kudi sosai, kowacce jam'iyya ma ta siya, su kansu wakilan jam'iyyun sun rinka sasantawa a tsakaninsu, idan wakilin wata jam'iyya a wata rumfa ya ga baza su kai labari ba sai ya sasanta da wanda yake da rinjaye a wannan wajen.''

Ya ƙara da cewa ''Ni da idona na ga ana siyar da ƙuri'a a kan Naira dubu uku, wasu wuraren naira dubu biyar, su jami'an tsaro saboda sun ga zaɓen na gudana cikin lumana sai suka mayar da hankalinsu zuwa tsakiyar jihar, ya kasance wasu wuraren ma idan ka je baza ka tarar da ko jami'in ɗan sanda daya ba.

Jami'in ya ƙara da cewa zaɓen ya gudana cikin lumana, don duk rumfar kaɗa ƙuri'ar da ka je za ka taras da mutane suna annushuwa suna farin ciki babu wata alamar fargaba, saboda kwanciyar hankalin da aka samu

''Tun da nake halartar zaɓe ban taba ganin inda aka jibge jami'an tsaro kamar wannan ba, shi yasa ma ƴan ƙungiyar IPOB suka janye matakin da suka ɗauka na hana zaɓen, domin sun lura cewa idan ma suka yi wani yunƙuri ba za su kai labari ba'' inji shi

To sai dai ya ce ''An samu matsala da na'urorin zaɓe, a wurare da yawa bayan an shirya an kammala komai ga kayan zaɓe amma na'urori suka ki tantance masu jefa ƙuri'a sai wajen yamma aka fara''.

A halin da ake ciki dai ana jiran ganin wanda zai lashe zaɓen, wanda yan takara goma sha takwas daga jam'iyyu daban-daban suka fafata.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN