Wani matashi dan shekara 34 ya kashe wani mutum bayan ya kama shi turmi tabarya yana lalata da matarsa, sakamakon haka ya mika kansa ga Yan sanda a garin Dedza da ke kasar Malawi. Shafin isyaku.com ya wallafa.
Mbungule Faisoni wanda ke kauyen Mchira da ke gundumar gargajiya na Kaphuka ya kashe Lembetsani Tchaison dan shekara 54, bayan ya kama shi turmi tabarya yana lalata da matarsa a cikin Lambu.
Kakakin yan sandan gundumar Dedza Cassim Manda, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce lamarin ya faru ne ranar 5 ga watan Nuwamba 2021.
Wani abokinsa ne ya rada wa Faison cewa ya gano Lembetsani Tchaison tare da matarsa a wani wajen shakataea. Sakamakon haka Faison ya hanzarta ya tafi wajen, amma.bai tarar da su ba.
Daga bisani ya tafi Lambun shi inda ya kama su suna tsaka da kwanciyar jima'i. Nan take suka tashi suka tsere bayan sun gan shi. Sai dai Faison ya bi Lambetsani da gudu, ya kama shi kuma ya sassare shi da adda, sakamakon haka ya mutu.
Bayan ya aikata kisan ne, sai ya tsere daga garin. Sakamakon haka yan sanda suka sanar da nemansa ruwa a jallo. Sai dai daga bisani, Faison ya mika kansa ga yansanda ranar Alhamis. Ya gaya wa yan sanda cewa yana fargaban cewa yan uwan Lambetsani za su kashe shi.
Reported by ISYAKU.COM
Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa
https://chat.whatsapp.com/
Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu LATSA NAN
Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari
Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari