An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8


Sai dai abun bakin ciki, an rasa wani Birgediya Janar da wasu jami’ai a yayin da suke kare kasarsu amma kuma rundunar sojin kasa da na sama suna ta tayar da ‘yan ta’addan ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai.

A wata sanarwa da ya saki a yammacin Asabar din, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojin, ya tabbatar da cewar yakin na nan yana gudana.

Ya ce baya ga kisan yan ta’addan, dakarun soji na nan sun lalata manyan motocin yakinsu da dama.

Ya ce:

"Dakarun hadin gwiwa, Operation HADIN KAI na arewa maso gabas, sun kashe mayakan ISWAP da dama a arangamar da suka yi a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.

Borno - Wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan ISWAP ne a halin yanzu suna musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.

Jama'a da dama sun tsere cikin daji yayin da wasu suka makale a gidajensu.

Adamu Saleh ya shaida wa The Sun cewa:

“Al’amarin ya yi muni amma ‘yan ta’addan sun janye a yanzu.”

Mazauna sun yi ikirarin cewa sun kai rahoton zirga-zirgar 'yan ta'addan ga jami'an tsaro amma ba a dauki wani mataki ba kafin wannan mummunar kungiyar ta afkawa garin Askira bayan sa'o'i.

Yayin da yake tabbatar da hare-haren, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Engr Abdullahi Musa Askira, ya shaida wa Daily Trust cewa a halin yanzu ‘yan ta’addan da sojoji suna musayar wuta.

A cewarsa:

“Eh, a halin yanzu ISWAP sun kai hari garin Askira. An sanar da ni cewa sojojinmu suna fafatawa da su, amma mazauna su tsere cikin daji.

"Mutane na sun gaya mani cewa maharan sun zo ne da motoci kusan 16 kuma ana cikin rudani a fadin garin a yanzu."

Wani jami’in sa kai na JTF, Yakubu Luka, ya ce nan take maharan suka far wa garin, inda suka tunkari sansanin sojoji.

"Muna sa ran samun tallafi daga al'ummar da ke kusa, yayin da nake magana da ku ana ci gaba da harbi da manyan bindigogi."

Yakubu yace:

“Muna kira ga hukumomi da su aika da jiragen yaki domin tallafawa sojojin kasa. An fi karfinmu; manyan motocin bindiga biyar ne kawai muke da su.”

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

A wani labarin, mazauna garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno sun tsere lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari wani kauye ranar Laraba.

Daily Trust ta ce ta samu labari daga majiyoyi cewa ‘yan ta'addan da suka kai harin da safe sun kona gidaje da dama.

Wani ganau ya ce maharan sun kai farmaki a yankin Krangla, mai tazarar kilomita takwas da garin.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu LATSA NAN

Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari 

Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN