Budaddiyar shawara ga yan Masarautar Zuru kan wanda ya kamata ku zaba shugaban karamar hukumarku


Bayan saukar da shugabannin kananan hukumomi guda 21 na fadin jihar Kebbi bayan kammala wa'adin mulkinsu bisa tanadin doka. Masani kan harkokin siyasar Masarautar Zuru da jihar Kebbi ya bayar da shawara kan irin wanda ya kamata mutanen Masarautar Zuru su zaba domin su shugabance su.

Shawarwarin su ne:

1. Zaben tsoho zai iya haifar da matsala. Idan aka zabi tsoho kuma ya ki idar da wakilci mai inganci. Zai iya neman a raga mashi saboda tsufansa alhalin shi ya ki ya martaba tsufarsa a fagen siyasa da aka samar domin al'umma.

2. Zaben mai izza zai iya jawo wa Masarautar Zuru asara a fagen siyasar jihar Kebbi.

3. Zaben wanda bai martaba matsayinsa har ya kai ga fada da na kasa da shi, har da lebarorinsa saboda rashin hakuri.

4. Zaben wanda ke fada da duk wani dan kasar Zuru ko a hada da shi domin a yaki dan kasar Zuru a kan harkar rashin gaskiya. 

5. Wanda ya taba rike wani mukamin Gwamnati kuma bai amfani yan Masarautar Zuru da komi ba.

6. Wanda a zahiri bai taba taimakawa matasa da jama'ar kasar Zuru ba ta fannin ilimi, kiwon lafiya ko ci gaban al'umma.

7. Wanda ke da sanannen Sana'a ko aikin hannu amma bai taba koya wa dan kasar Zuru sana'ar ba. 

8. Wanda bai jin kunyan yin karya ga al'umma.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN