Da dumi: Mun mayar wa da CBN N19.3bn ta albashin Kogi da Bello ya boye, EFCC


Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta mayar da N19.3 biliyan kudin jihar Kogi wanda gwamnatin jihar ta boye zuwa babban bankin Najeriya. 

Hukumar tun farko ta sanar da yadda mulkin Gwamna Yahaya Bello ya kwashe kudin tare da dankara su a wani asusun banki, Daily Trust ta ruwaito. 

Daily trust ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kogi ta musanta boye kudin inda ta zargi EFCC da zabga karya.

Amma a takardar da Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ya fitar, ya ce kudin an mayar da su zuwa babban bankin Najeriya.

"Babban bankin Najeriya ya amsa samun kudi har N19.3 biliyan wanda EFCC ta samo daga gwamnatin jihar Kogi bayan ta boye su a asusun wani banki. Wannan sai ya dakatar da gangami tare da musun da gwamnatin jihar ke yi na cewa babu wani kudi da aka samo daga wurin ta."

"A wata wasika mai kwanan wata 9 ga Nuwamban 2021, babban bankin Najeriya ya sanar da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, cewa sun samu kudin," yace.

Wani bangare na wasikar ya ce:

"Mayar da kudin ya zama biyayya ga hukuncin wata babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jihar Legas na ranar 15 ga Oktoban 2021 inda kotun ta umarci a saki asusun bankin yadda za a iya mika kudin zuwa CBN. Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ne ya bayar da umarni.

"Hukumar ta sanar da kotun cewa,hukumar bankin da kudin ya ke ta tabbatar da wanzuwarsu."

Zargin damfarar N2bn: EFCC ta garkame kadarorin tsohon daraktan sojin ruwa

Source: Legit

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE