An sami gawakin wasu matasan ma'aurata a cikin ban dakin gidansu a birnin Akure na jihar Ondo. Shafin isyaku.com ya samo.
An sami gawar Akinro Blessing Ojay tare da na matrashi Mary Igwe ranar Talata 23 ga watan Nuwamba.
Shafin isyaku.com ya gano cewa alamu da aka gani a jikin gawakin ma'auratan sun nuna cewa an kashe su ne aka kai gawakinsu a cikin ban dakin gidansu aka kulle.
Makwabta sun kula cewa basu gan ma'auratan ba har tsawon wani lokaci. Sakamakon haka aka sanar da yansanda wanda suka gano abin da ya faru kuma suna ci gaba da bincike kamar yadda isyaku.com ya tattaro .
Ma'auratan sun yi aure da kananan shekaru kuma suna matukar kaunar junansu kafin a kashe su.
Rubuta ra ayin ka